MUHIMMAN DARUSSA GA AL’UMMAR MUSULMI
MUHIMMAN DARUSSA GA AL’UMMAR MUSULMI
  | لغة الهوسا   | 1019

MUHIMMAN DARUSSA GA AL’UMMAR MUSULMI

NA

SHEIK ABDULAZIZ BN ABDALLAH BIN BAZ

FASSARA ATAKAICE

DAGA

SA’IDU ALIYU MAIKWANO GUSAU,

ZAMFARA STATE NIGERIA

MATASHIYA

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikkai, karshen kwarai ya tabbata ga masu takawa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga bawansa manzon sa, Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka wadannan bayanaine takaitattu akan ababen daya wajaba kowane musulmi ya sani game da addinin sa na musulunci. Na sanya masa suna Muhimman Darussa Ga Al’ummar Musulmi

Ina rokon Allah ya amfanar da dukkan musulmi da shi yakuma karbar mani wannan aiki domin shi mai baiwa ne mai karimci.

SHEIK ABDULAZIZ BN ABDALLAH BIN BAZ

DARASI NA FARKO

KOYON FATIHA DA WASU KANANAN SURORI

Wajibine ga kowane musulmi ya koyi karatun Suratul Fatiha da gajerun surori tun daga Suratul Zalzala zuwa Suratu Nasi daga malami yakuma haddacesu tareda sanin wani abu daga maanoninsu.

DARASI NA BIYU

RUKUNNAN MUSULUNCI

Sanin rukunnan musulunci guda biyar tare da sanin sharuddan kalmar ‘Lailaha illallah. Ma’anar ta kuwa itace kore bauta ga duk wanda ba Allah ba tare da tabbatar da ita gareshi kawai batare da abokin taraiya ba.

Sharuddan kalmar Lailahaillallah gasu kamar haka:-

a. Ilimi mai kore jahilci

b. Yakini mai kore shakku

c. Ikhlasi mai kore shirka

d. Gasgatawa mai kore karyatawa

e. So mai kore kiyaiya

f. Jawuwa mai kore bijirewa

g. Karba mai kore ki

Dakuma kafircewa duk wani abu da ake bautawa wanda ba Allah ba. Sai kuma sanin ma’anar kalmar Muhammadu rasulullah wanda shine imani dashi, gasgatashi cikin dukkan labaran daya bayar yimasa da’a ga abunda yayi umurni dakuma nisantar abubuwan da ya hana kada kuma abautawa Allah saida abunda ya shar’anta.

Sannan sanin sauran rukunnan musulunci guda hudu da suka hada da sallah Azumi, Zakka da Aikin Hajji.

DARASI NA UKKU

RUKUNNAN IMANI

Rukunnan Imani shidda (6) ne kamar haka:-

1. Imani da Allah

2. Imani da Malaikunsa

3. Imani da Manzaninsa

4. Imani da Littafansa

5. Imani da Ranar Lahira

6. Imani da Kaddara ta alhairi da ta sharri dukkansu daga wajen Allah ne.

DARASI NA HUDU

SANIN KASHE – KASHEN TAUHIDI DA SHIRKA

Tauhidi yakasu kashi ukku kamar haka:-

(a) Tauhidin Rububiya: Shine imani da cewa Allah shine mahaliccin komi, shi kuma ke tafiyar da komi batare da abokin taraiya ba.

(b) Tauhidin Uluhiya: Imani da cewa Allah shi kadaine abun bauta na gaskiya bayada abokin taraiya kuma wannan itace ma’anar Lailaha illallah.

(c) Tauhidin Asma’u Wassifat: Imani da duk abunda yazo daga Al’qurani maigirma da ingantattun hadisan Manzon Allah (S.A.W) game da sunaye da siffofin Allah batare da batawa ko juyar dasu daga ma’anonin suba.

KASHE KASHEN SHIRKA: Shirka ta kasu kashi Ukku kamar haka:-

(a) Babbar Shirka: Itace abunda ke rusa aiki dakuma tabbatarda ma’abocinta a cikin wuta. Misalin ta sun hada da kiran matattu, rokonsu, da yin alwashi ko yanka don su.

(b) Shirka Karama: Itace riya acikin ayukka ko rantsuwa da wanin Allah dakuma cewa in Allah ya yarda wani ya yarda, da dai sauransu.

(c) Boyaiyar Shirka: Itace kamar mutum ya kyautata sallah ko wata ibada da yakeyi domin ganin idon mutane.

]

DARASI NA BIYAR

AL-IHSAN

Ihsan shine kabautawa Allah kamar kana ganin sa idan ka kasance baka ganin sa to shi yana ganin ka.

DARASI NA SHIDDA ZUWA NA GOMA SHAHUDU

SHARUDDAN SALLAH

Wajibine ga kowane musulmi yanemi sanin sharuddan sallah, rukunnan sallah, wajiban sallah, sanin yadda ake tahiya, sunnonin sallah, abubuwan dake bata sallah, sharuddan alwalla, farillai, sunnani da kuma abubuwa dake walwale alwalla.

DARASI NA GOMA SHABIYAR

DABIANTUWA DA KYAWAWAN DABIU NA SHARIA

Ya wajaba ga kowane musulmi da ya dabi’antu da kyawawan dabi’u na sharia kamar gaskiya, rikon amana, kunya, sadaukantaka, karimci, cika alwawari dakuma nisanstar duk abunda Allah ya haramta, da kyautata dangantaka tsakanin ka da makwabta, taimakawa mabukata da dai duk sauran dabiu na gari da addinin musulunci yake kira zuwa garesu.

DARASI NA GOMA SHA SHIDDA

LADUBBAN MUSULUNCI

Ya wajaba ga kowane musulmi ya siffantu da ladubban musulunci kamar sallama, sakin fuska, kula da ladubban cin abinci da shan abunsha, gaida wanda yayi atishawa, gaida marasa lafiya, bin jana’iza, kiyaye ladubban shiga da fita masallaci, ladubban shiga da fita gida, ladubban tafiya, ladubban hulda da mahaifa, yanuwa, yara da manya da makwabta da kuma ladubban sanya tufafi da dai sauransu.

DARASI NA GOMA SHA BAKWAI

NISANTAR SHIRKA DA DUKKAN AYUKKAN SABON ALLAH

Ya wajaba ga kowane musulmi ya gujewa shirka da sauran naukkan sabon Allah daban daban musamman ayukka guda bakwai da ke kai mutun wuta. Sunkuwa hada da shirka da Allah, sihiri kisan kai, cin riba cin dukiyar maraya, gudu a fagen fama dakuma yiwa matan aure muminai kabafi.

Misalin sauran naukkan sabo sun gada da sabawa iyaye, yanke zumunta, shedar zurantsuwar karya, cutar da makwabta, zaluntar mutane, shangiya, caca, giba, annamimanci da dai sauran laifukan da Allah da manzonsa sukayi hani akan su.

DARASI NA GOMA SHA TAKWAS

SANIN HUKUNCE HUKUNCEN JANA’IZA

Ya wajaba ga musulmi yasan hukunce hukuncen jana’iza kamar hukunce hukncen jinya, wankan gawa, likkafani, sallar janaiza, bizne gawa dakuma ziyarar makabarta.

Wannan shine karshen abunda ya saukaka na abubuwan da na harhada gameda wadannan muhimman darussa da yawajaba ga kowane musulmi ya sansu. Tsirar Allah da amincin sa su tabbata ga Annabin mu Muhammadu da Alayensa da Sahabban sa.

MUHIMMAN DARUSSA GA AL’UMMAR MUSULMI

اترك تعليقاً

لن يتم نشر عنوان بريدك الإلكتروني. الحقول الإلزامية مشار إليها بـ *