MATSAYIN YANAR GIZO TA TUTAR SALAF
MATSAYIN YANAR GIZO TA TUTAR SALAF
  | لغة الهوسا   | 2292

MATSAYIN YANAR GIZO TA TUTAR SALAF

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hakika godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa muna neman taimakonsa muna neman gafararsa, muna kuma neman tsari daga sharrin kawunanmu da miyagun Ayyukanmu, wand aAllah ya shiryar dashi babu mai batar dashi, wanda kuma ya batar babu mai shiryar dashi, ina saida babu abun bautawa da gaskiya (bisa ga can-canta) sai Allah bay a da abokin tarayya. Ina kuma shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsane.

Yaku wadanda sukayi imani! Ku bi Allah da takawa akan hakkin binsa da takawa, kuma kada ku mutu face kuna masu sallamawa (musulmi) (Ali imrana: 102)

Yaku mutane! Kubi ubangijinku da takawa wanda ya kalittaku daga rai guda kuma ya halitta daga gareshi Ma’aura tansa, kuma ya watsa daga garesu maza masu yawa da mata. Kuma kubi Allah da takawa, wanda kuke tsoron juna da (sunan) shi, da kuma zumunta. Lallene Allah ya kasance akanku mai tsarone.(Nisa’i:1)

Ya ku wadanda sukayi imani! Kubi Allah da takawa, kuma ku fadi Magana madaidaiciya, ya kyautata muku ayyukanku, kuma ya gafarta zunubanku, kuma wanda yayi da’a ga Allah da manzonsa to lalle ya rabbanta, babban rabo mai girma. (Ahzab:70-71)

Bayan haka ina godewa Allah mai karimci abin godewa akan kyawawan datarwarsa ga tsayarwa da bude wannan shafin yanar gizo (TUTAR SALAF A SUDAN). Ina rokon Allah ya sanya wannan shafin yanar gizo ya karba sunan sa ta hanyar zama tutar gaskiya da ilimi da Alheri akan tafarkin manzon Allah (SAW): bisa fahimtar magabata na gari Allah ya yarda dasu gaba daya, ya tsayar damu acikinsu gobe kiyama da falalarsa da baiwarsa. Kuma muna fatar wannar tuta ta zama mahallin amfani ga “yan uwa musulmi maza da mata, matasa da tsofaffi na kasar sudan da najeriya dama sauran kasashen duniya baki daya.

Zamuyi aiki da izinin Allah da datawarsa kafada-dakafada da “yan uwanmu daliban ilimi wadanda ke kula da wannan shafi na yanar gizo domin hada kan al’ummar musulmi da tushen addini su a musulunci wanda ya hada littafin Allah da sunnar manzonsa (saw) akan fahimtar magata na gari da kuma tabbatar da wajabcin hada alka ta hakika da malaman salaf, malaman Allah. Da fatar Allah ya kiyayea rayuwarsu ya kuma jikan matattunsu. Ina kuma rokon Allah (swt) da kyawawan sunayensa da madaukakan siffofinsa day a taimakemu wajen daga wannan tuta da daukarta da kuma bayar dad a hakkinta da fuskar da yake yarda da ita har zuwa lokacin da zamu gamu dashi, ya kuma sakawa duk wanda ya bada gudun mawa ta wannan hajin da alheri, a farkon wannan aiki, a tsa kiyar sa da karshensa, Kuma Allah ya kyautata niyyarmu, kada ya barmu da dabarunmu koda kyabtawar ido, karshen addu’armu godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikkai.

Nazzar bin Hashim Abbas

Tsohon dalibin jami’ar madinar Annabi

Mai kula da wannan shafi na

Yanar gizo a sudan

13 muharram 1424 A.H

28th November, 2012

المترجم

Me tarjama sa’id Aliyu mai kwano

Imam masjid sahaba, gusau

Zamfara state, Nigeria

اترك تعليقاً

لن يتم نشر عنوان بريدك الإلكتروني. الحقول الإلزامية مشار إليها بـ *