Wasiya ga musulmin najeriya Daga Sheikh (Dr) Muhammad bin hadi Alamadkwali
Wasiya ga musulmin najeriya Daga Sheikh (Dr) Muhammad bin hadi Alamadkwali
  | لغة الهوسا   | 706

Wasiya ga musulmin najeriya

Daga

Sheikh (Dr) Muhammad bin hadi Alamadkwali

Allah ya kiyaye shi, ya tabbatar dashi akan musulunci da sunna ya kuma saka masa da mafificin alkhairinsa.

Wadda ya gabatr daren lahadi 20 rabiu Auwal 1433

Akan abubuwan da bokoharam suke yin a kafirtarwa, tada bamabamai da sauran muhimman batutuwa daban daban.

Muna rokon Allah mai girma da daukaka ya amfanar da musulmin najeriya dama sauran musulmi akoina a doran kasa da wannan wasiyya.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godiya ta tabba tag a Allah ubangijin talikai, tsira da aminci su tabba tag a annabi mhammad da alayensa da sahabbansa da sauran mabiyansu da kyautatawa.

Ina wasiya ga ‘yan uwa na ‘ya’ya na musamman a najeriya da ko’ina a duniya saboda tambayar da akayi mini game da ‘yan bokoharam wadanda sukabi tafarkin khawrijawa bangaren kafirtawa da zubar da jinni.

Da farko zance wannan tafarki sam musulunci bai yarda dashiba kuma baida wata madogara a cikinsa domin wannan ba shine tafarkin manzanniba. Tafarkin manzanni shine bushara da gargadi kamar yadda Allah mai girma da daukaka yace:

“manzanni  masu bayar da bushara kuma masu gargadi domin kada wata hujja ta kasance ga mutane akan Allah bayan manzanni, kuma Allah ya kasance mabuwayi kuma mai hikima”.(nisa’i:165)

Da kuma cewar Allah ga Annabinsa :

Ya kai Annabi! Lalle mu mun aikoka kuma mai shaida, kuma mai bayar da bushara kuma  mai gargadi, kuma mai kira zuwa ga Allah da izininsa, kuma fitila mai haskakawa”. (Ahzab45-46)

Abunda wannan aya ta kunsa shine tafarkin da’awar annabi (saw) don haka Allah (swt) yace:

“kace: wannan ce hanyata ina kira zuwa ga Allah bisa basira, nida wanda suka bini kuma tsarki ya tabbata ga Allah, ni kuma ban zama daga masu shirkaba”. (Yusuf:108)

Wannan itace da’awar manzon Allah (saw) watau kira zuwa ga Allah domin shiryarda mutane, domin fitar dasu daga duhu zuwa ga haske da kubutar dasu daga shirka zawa tauhdi daga jahilci zuwa ilimi, wanda yayi irin wannan da’awar shine wanda yabi manzon allah (awt) yace:

“kace: idan kun kasance kuna tsoron Allah to, ku bini Allah ya soku” (Ali imrana:31)

Ina tsoratar da ‘yan uwa na da ‘ya ‘ya na a najeriya dasu guji sabawa wannan tafarki, domin irin wannan yana baiwa makiya kafar samun nasara ga musulmi kuma ina maku wasiyya da ku rika tuntubar gogaggun malaman sunna musamman malaman saudiya saboda gogewarsu a tafarin da’awa dai-dai da sunna kamar su ibn baz, bin Uthaimin, Albani da dai sauransu.

Haka ma kuyi kokarin hada kai da tsofaffin daliban jami’ar islamiyya ta madina domiin sun samu horaswa ta musamman game dad a”wa akan tafarkin sunna, musamman wadanda suka dore akn wannan tafarki. Ku kuma nisan ci yin tarayya da duk wasu wadanda suka siyasar da da’awar musulunci. Kuci gaba da koyar da jama’a akidar musulunci (tauhidi) ingantatta akan tafarkin sunna domin Annabi ya zauna a madina tsawon shekara goma sha ukku yana kira zuwa ga tauhidi. Ku zabi kananan litatta fan tauhidi ku rinka karantar da mutane su a masallaci da sauran wuraren haduwar jama’a ku shiga shafikan yanar gizo wadanda domin kuga yanda malamai suka yi shirin kananan litattafan tauhidi kamar: ALKAWA’IDUL ARBA’A ADDURUSUL MUHIMMA,SALASATUL USUL, AL-AKIDATUL WASIDIYYA DA TALKHISUL HAMAWIYYA          Wadanda manyan malaman sunna sukayi kamar bin baz, bin Uthaimin, Alfauzan da Albani da dai sauran ire-irensu. Ku karan tar dasu ga ‘yan uwanku da ‘ya ‘yanku ‘yan najeriya.

Kuma ku sani jahadi baya zamowa jahadi fisabilillahi sai idan anyishi akan tafarkin sunna kuma tarihin manzon Allah (SAW) ya nuna mana matkan daya bi kafin yayi jahadi da kuma yadda yayi jahadi.

A karshe, ina yi muku kashedi dab akan kungiyuyin addini da suka shigo kasarku domin domin irin wadannan kungiyoyi kan sanya shigar Ahlissunna (salafiyya) domin su batar daku, muna Rokon Allah ya karemu ya kareku, ya tabbatar damu daku akan tafarkin magabata a dukkan bangarorinsa. Tsiran Allah da amincinsa su tabbata ga bawansa manzonsa Muhammad da alayensa da sahabbansa da mabiyansa. Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.

المترجم

Mai tarjama sa’ad Aliyu mai kwano

Imam masjidussahaba, Gusau

Zamfara state, Nigeria.